An yanke wa tsohon shugaban kasar Peru Martin Vizcarra hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari

An yanke wa tsohon shugaban kasar Peru Martin Vizcarra hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari

Wata kotu a kasar Peru ta yankewa tsohon shugaban kasar Martin Vizcarra hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari saboda samunsa da hannu a badakalar cin hanci da rashawa lokacin da yake gwamnan yankin kudancin Moquegua.

A hukuncin da ta yanke a ranar Laraba, kotun ta kuma hukunta Vizcarra da dakatar da shi na tsawon shekaru 9 daga tsayawa takara, da kuma tara.

Ana sa ran zai fara zaman gidan yarin nan take. Amma Vizcarra ya nuna yana shirin daukaka kara kan hukuncin da aka yanke masa.

"Wannan ba adalci bane, ramuwar gayya ce," Vizcarra ya rubuta a shafukan sada zumunta yayin mayar da martani ga hukuncin. "Amma ba za su karya ni ba."

An same shi da laifin karbar cin hancin da ya haura dala 600,000 domin bada kwangilar gudanar da manyan ayyuka a Moquegua.

Vizcarra, a halin yanzu jagora a jam'iyyar Peru ta farko, ya jagoranci Moquegua daga 2011 zuwa 2014 kafin daga bisani ya zama shugaban kasa daga shekaran 2018 zuwa 2020.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: