Sanata Natasha ta shiga ofishinta bayan dakatawar watanni 6 da majalisar Dattawa ta yi Mata.

Sanata Natasha ta shiga ofishinta bayan dakatawar watanni 6 da majalisar Dattawa ta yi Mata.

Majalisar Dattawan Najeriya ta bude Ofishin Sanata mai wakiltar kogi ta tsakiya Natasha Akpoti-Uduaghan bayan ya shafe watanni 6 a garkame tun bayan da Majalisar ta dakatar da ita bisa samunta da laifin kazafi ga Shugaban Majalisar Dattawan Sanata Godswill Akpabio na yin lalata da ita.

Tun a Ranar 6 ga watan Maris ne Majalisar ta yanke mata hukuncin dakatarwa har na tsawon watanni shida daga shiga Majalisar.

Duk da daukaka Kara da Sanatan tayi zuwa babban kotu dake Abuja inda Mai shari’a a babbar kotun tarayya da ke Abuja, Binta Nyako, a watan Yuli, ta bayyana cewa dakatarwar da aka yi mata na tsawon watanni shida a matsayin wuce gona da iri kuma ba bisa ka’ida ba, 

sannan ta umarci majalisar dattijai da ta dawo da Sanatan bakin aiki, amma duk da haka majalisar tayi burus da hukuncin kotun sai da watanni shidan suka cika.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: