Mai tsaron ragan tawagar Mata ta Kungiyar kwallon kafar Najeriya, Super Falcons Chiamaka Nnadozie tazo ta hudu a kyautar Balllon d'or da ake zabar mata masu tsaron raga 5 da suka nuna bajinta a kowane shekara.
Mai tsaron ragar Kungiyar kwallon kafar Ingila da Chelsea, Hannah Hampton ce tazo ta daya yayin da Ann-Katrin Berger Mai tsaron ragar tawagar Jamus ta zo ta 2 sai Cata Coll ta kasar Sipaniya a matsayi na uku yayin da Chiamaka Nnadozie ke mataki na hudu sai Daphne van Domselaar Mai tsaron ragar Netherlands a matsayi na 5.
An gudanar da bikin bayar da kyautar ne a daren jiya litini a birnin Paris na kasar Faransa kamar yadda aka saba gudanar, inda Dan wasan PSG da faransa Ousmane Dembele ya lashe kyautar Balllon d'or a bangaren maza yayin da 'yar wasan Kungiyar kwallon kafar Mata ta Barcelona da Sifaniya, Aitana Bonmati ta lashe kyautar a bangaren Mata karo na uku.
.jpeg)
0 Comments:
Post a Comment