Kotu ta samu ba Amurke, Ryan Routh da laifin yunkurin kashe Shugaban Amurka Donald Trump

Kotu ta samu ba Amurke, Ryan Routh da laifin yunkurin kashe Shugaban Amurka Donald Trump

Kotu ta samu ba Amurke, Ryan Routh da laifin yunkurin kashe Shugaban Amurka Donald Trump a Florida a Watan Satumban bara.

Wata kotu a Amurka ta samu Ba’amurken nan Ryan Routh da laifin yunkurin kashe shugaba Amurka Donald Trump a watan Satumban shekaran da ta gabata a kusa da filin wasan golf na Trump a  Florida, kamar yadda babban mai shigar da kara na Amurka Pam Bondi ya sanar a shafinsa na sada zumunta. 

Alkalin kotun da aka yi Shari'ar ya gano cewa Ryan Routh, mai shekaru 59, ya yi niyyar kashe Trump, wanda a lokacin yana matsayin tsohon shugaban kasa ne kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Republican. 
Shaidu sun tabbatar da cewa an hango shi yana saita Trump din da bindiga ta wani shinge a lokacin da Trump ke wasan golf a gidan wasan Golf na Trump International da ke West Palm Beach. 

An kuma same shi da laifi kan wasu tuhume-tuhume guda hudu da suka hada da wahalar da jami’in gwamnati da kuma laifukan mallakan makamai. 
Zai iya fuskantar hukuncin daurin rai da rai a gidan yari matukar aka tabbatar da hukuncin.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: