Dan asalin Najeriya mai shekaru 63 ya samu damar ci gaba da zama a Birtaniya bayan ya shafe shekaru 39 a can.
Hukumomin kasar sun yi yunkurin dawo da shi gida Najeriya duk da hallin rashin lafiyan da yake fama da shi, lamarin da yasa ya shigar da Kara a kotu inda ya sanar da alkalin kotun cewa ba shi da wasu dangi da ya sani yanzu a Najeriya.
Mutumin mai suna Olubunmi George ya bar Najeriya ne tun a shekaran 1986 a lokacin Yana da Shekaru 24, Kuma tun wancan lokacin bai sake komawa Najeriyan ba.
Ya sanar da kotun cewa ya samu rashin lafiya na shanyewar jiki har sau biyu Kuma duk abokansa da iyalinsa dake Nan Birtaniya ne suka kula da shi.
Bayan hukuncin ya sanar da manema labarai cewa yanzu ya samu natsuwa da kwanciyar hankali domin cigaba da rayuwarsa kamar yadda ya saba.

0 Comments:
Post a Comment