Karancin Albashi ke sanya Likitoci barin kasar nan, inji NARD

Karancin Albashi ke sanya Likitoci barin kasar nan, inji NARD

Kungiyar Likitoci mazauna Najeriya tace Karancin Albashi ke sanya Likitoci barin kasar.

Shugaban Kungiyar, Dr Tope Osundara ne ya baiyana hakan a lokacin da yake jawabi a taron Kungiyar na 45 a jihar Katsina. 

Inda ya kara da cewa baya ga karancin Albashi, karanci ma'aikata masu kula da fannoni daban-daban na kiwon lafiya da karancin kayan aiki wanda ke sa yawaitan marasa lafiya a asibitoci na daga cikin abubuwan dake sanya kwararrun likitocin kasar nan yin kaura zuwa Kasashen ketare.

Sai dai a nashi jawabin, Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya yi kira ga kwararrun likitocin da su fifita kishin kasa fiye da samun kudi.

Radda ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa dukkan likitocin jihar, da inganta rayuwarsu, da tabbatar da samar da ayyuka masu inganci.

Ya ci gaba da cewa, “Muhimmancin aikin likitanci ya sa kowace al’umma na bukatarsa, don haka ya kamata ku ma ku sanya kishin kasa a gaba a kan albashi, saboda muhimmiyar rawar da kuke takawa wajen yi wa rayuwar al’umma hidima tana da matukar muhimmanci, ta yadda ita ma tana bukatar jin kai.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: