Jawabin Shugaban kasar Iran a zauran majalisar dinki duniya karo na 80

Jawabin Shugaban kasar Iran a zauran majalisar dinki duniya karo na 80

Shugaban kasar Iran, Pezeshkian ya gabatar da jawabi a zauran majalisar dinki duniya inda yayi kakkausar suka akan Israi'la game da Kisan kiyashin da take yi a Gaza da kaddamar da hare-hare akan makwabtanta da yunkurin fadada haramtacciyar kasar ta Israi'la.

Pezeshkian ya ce harin baya-bayan nan da kasar Israi'la ta kai kan makwabtanta ya nuna cewa Isra'ila ba ta da sha'awar samar da zaman lafiya ta hanyar daidaitawa da kasashen yankin cikin lumana.

Inda yace maimakon hakan Israi'la da masu daukar nauyinta sun zabi su yi amfani da karfi wajen gamsuwa da abun da suka yi amanna da shi.

Shugaban na Iran ya kuma yi Allah wadai da kalaman da jami'an Isra'ila ke yi na kokarin kafa "Isra'ila mafi girma" (greater Is'rael), wanda aka fassara da nufin samar da cikakken iko a kan yankin Falasdinawa da aka mamaye da kuma samar da wuraren da ake kira "buffer" a cikin kasashen da ke kewaye da ita.

Haka zalika Pezeshkian ya nanata abin da ya ce shi ne matsayar Iran na tsawon lokaci game da shirinta na nukiya wace ta kasance ta zaman lafiya ce: 

inda ya ce, "Ina sake nanatawa a gaban wannan majalisa cewa Iran ba ta taba neman ba kuma ba za ta taba neman kera makamin nukiliya ba."




SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: