An yankewa Sojoji uku hukuncin daurin rai da rai bisa laifin sayar da makamai ga 'yan ta'adda.


Wata kotun sojin Najeriya ta musamman da ke zamanta a Maiduguri a jihar Borno ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga wasu sojoji uku da kuma cikon na hudunsu daurin shekaru 15 bisa samun su da laifin sayar da makamai ba bisa ka'ida ba tare da hadin gwiwar jami'an 'yan sanda ga kungiyoyin 'yan ta'adda.

Birgediya Janar Ugochukwu Unachukwu, mukaddashin kwamandan runduna ta 7 kuma kwamandan sashi 1, Operation Hadin Kai (OPHK) ne ya jagoranci shari’ar. An gudanar da shari'ar ne a hedikwatar rundunar da ke Maiduguri.

Da yake zartar da hukuncin, Birgediya Janar Mohammed Abdullahi, Shugaban Kotun Sojin, ya samu Sajan Raphael Ameh, Sajan Ejiga Musa, da Lance Kofur Patrick Ocheje da laifin da aka tuhume su da shi kuma ya yanke masu hukuncin daurin rai da rai a gidan yari.

Sai Kofur Omitoye Rufus, wanda aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: