Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya kai ziyara Jihar Borno domin jajanta wa sojoji da kuma iyalan waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon wani hari da aka kai a jihar.
Shettima ya isa Borno ne bayan rahotannin hare-hare da suka yi sanadiyyar asarar rayuka da jikkata mutane da dama, inda ya gana da jami’an tsaro da kuma masu jinya a asibitoci.
A yayin ziyarar, ya bayyana ta’aziyyarsa ga sojoji da gwamnatin jihar, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da tallafa wa sojoji da kuma ƙara ƙaimi wajen magance matsalar tsaro a yankin Arewa maso Gabas.
Ya kuma yi kira da a haɗa kai tsakanin al’umma da hukumomin tsaro domin dakile hare-haren ‘yan ta’adda, yana mai cewa gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.
Rahotonni sun nuna cewa ziyarar ta Shettima na cikin matakan gwamnatin tarayya na nuna goyon baya ga dakarun da ke fuskantar matsin lamba a yankin.

0 Comments:
Post a Comment