Rahotanni sun bayyana cewa likitar ta haihu cikin nasara a wani asibiti a Bayelsa, inda ta haifi jarirai uku lafiya. Sai dai bayan haihuwar, ta samu matsalolin lafiya da suka biyo baya, wanda ya yi sanadin rasuwarta.
Dr. Ere Ogbachi ta kasance likitar mata da haihuwa (Obstetrics and Gynaecology) wadda ke kula da mata masu juna biyu da haihuwa.
An ruwaito cewa jariran duk suna raye kuma suna cikin koshin lafiya bayan haihuwar.
Lamarin ya tayar da hankula da jimami a tsakanin jama’a, inda mutane ke nuna tausayi da addu’a ga marigayiyar.

0 Comments:
Post a Comment