Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Sojojin Amurka za su cigaba da kasancewa Kusa da Iran Har sai An Cimma “Yarjejeniya ta Gaske”.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Sojojin Amurka za su cigaba da kasancewa Kusa da Iran Har sai An Cimma “Yarjejeniya ta Gaske”.

Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa sojojin Amurka, ciki har da jiragen ruwa da jiragen sama da dakarun ƙasa za su ci gaba da kasancewa a yankin da ke kusa da Iran har sai an kammala cikakken yarjejeniya da Ƙasar Iran. 
Wannan sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake cigaba da samun shakku daga bangarorin biyu game da sharuɗɗa da Yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta kunsa.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a dandalin sa na Truth Social, Trump ya ce: “Duk jiragen ruwa, jiragen sama, dakarun soji da duk wani kayan aiki da ya dace za su kasance a yankin dake kusa Iran har sai an aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar da aka cimma.” 
Ya kuma ƙara da cewa idan hakan bai faru ba, Amurka za ta iya komawa kaddamar da manyan hare‑hare da suka fi na da ƙarfi fiye da kowane abin da aka taɓa gani. 

Rahotanni sun nuna cewa akwai bambance‑bambance tsakanin bangarorin biyu musamman dangane da shirin nukiliyar Iran, inda Trump ya sake jaddada cewa Iran bata da damar mallakar makaman nukiliya. 
A gefe guda, majalisar ƙolin Iran ta ce tana da ikon ci gaba da samar da uranium a ƙarƙashin sharuɗɗan tsagaita bude wutan da aka cimma. 

Masu sharhi na duniya sun nuna cewa wannan jawabi na Trump na iya ƙara jefa yankin cikin wani mawuyacin hali — musamman ma da yake akwai harin sojoji da ke ci gaba a wasu sassan yankin, ciki har da harin Isra’ila a Lebanon, wanda ya halaka mutane da dama kuma ya ƙalubalanci yunkurin tsagaita bude wuta. 

Har yanzu ana sa ran tattaunawar zaman lafiya za ta ci gaba a mako mai zuwa, tare da ƙoƙarin samar da yarjejeniya mai ɗorewa tsakanin Amurka da Iran don kawo ƙarshen rikicin gaba ɗaya. 

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: