Sojojin Isra’ila Sun Ce Dan Jaridar Al Jazeera da aka Kashe a Gaza Yana aiki tare da Hamas ne.

Sojojin Isra’ila Sun Ce Dan Jaridar Al Jazeera da aka Kashe a Gaza Yana aiki tare da Hamas ne.

Sojojin Isra’ila sun bayyana cewa dan jaridar Al Jazeera, Mohammed Wishah, wanda suka kashe a Gaza ranar 8 ga Afrilu, 2026, yana daga cikin mayakan Hamas. Hukumar ta ce Wishah yana aiki ne a matsayin dan jarida amma yana cikin ayyukan samar da makamai da Hamas ke harbawa zuwa cikin Isra’ila.

An kashe Wishah ne lokacin da harin jirgin sama mai saukar ungulu na Isra’ila ya nufi motar da yake ciki a yammacin birnin Gaza, inda ya mutu a nan take.

Sai dai Al Jazeera ta yi tir da ikirarin Isra’ila, inda ta bayyana cewa Wishah yana aikin jarida ne kadai a lokacin harin. 
Haka zalika Kungiyoyin kare ‘yancin ‘yan jarida sun bayyana kashe dan jaridan a irin wannan yanayi a Matsayin babban laifi  a karkashin doka ta kasa da kasa.

Wannan lamari ya kara tada hankalin duniya kan hanyoyin da ake bi wajen tabbatar da kariya ga ‘yan jarida a rikicin Gaza, inda aka samu wasu ‘yan jarida da dama sun rasa rayukansu a wannan rikici.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: