‘Yan Sama Jannati Artemis II, Sun dawo Duniya Bayan Tafiya zuwa duniyar Wata Mai cike da Tarihi.

‘Yan Sama Jannati Artemis II, Sun dawo Duniya Bayan Tafiya zuwa duniyar Wata Mai cike da Tarihi.

Shirin hukumar kula da sararin samaniyar ƙasar Amurka NASA mai suna, Artemis II ya kammala tafiya mai tarihi bayan ‘yan sama jannati huɗu sun dawo wannan Duniyan cikin nasara, bayan sun zagaya duniyar Wata a wani aiki da ya ɗauki kusan kwanaki 10.

Jirgin sararin samaniyar mai suna Orion ya sauka cikin Tekun Pasifik kusa da gabar California, inda jami’an sojin ruwa na Amurka suka tarbi jirgin tare da ɗaukar matakan dawo da ‘yan sama jannatin.

Wannan shi ne karo na farko cikin sama da shekaru 50 da mutane suka yi tafiya zuwa kusa da Wata, tun bayan shirin Apollo a shekarar 1972.

‘Yan sama jannatin su ne: Reid Wiseman, Victor Glover, Christina Koch, da Jeremy Hansen daga Kanada. Sun yi tafiya mafi nisa da ɗan adam ya taɓa yi a sararin samaniya, kuma sun gwada sabbin fasahohin jirgin Orion domin shirin saukar ɗan Adam a duniyar Wata a nan gaba.

NASA ta bayyana wannan nasara a matsayin muhimmin mataki zuwa shirin Artemis na gaba, wanda ke nufin kafa tushe na dindindin a duniyar Wata da kuma shirye-shiryen zuwa duniyar Mars.

A cewar rahotanni, saukar jirgin ta kasance cikin nasara sosai duk da ƙalubalen sake shigar jirgin cikin sararin samaniyar Duniya, inda aka yi amfani da leman sama (parachute) don rage gudun sa kafin saukarsa lafiya cikin teku.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: