Mutane 6 ne suka mutu yayin da 29 suka jikkata a wani mummunar hatsarin mota da ya faru akan hanyar Legas zuwa Ibadan

Mutane 6 ne suka mutu yayin da 29 suka jikkata a wani mummunar hatsarin mota da ya faru akan hanyar Legas zuwa Ibadan

Mutane 6 ne suka mutu yayin da 29 suka jikkata a wani mummunar hatsarin mota da ya faru akan hanyar Legas zuwa Ibadan.

A kalla mutane shida ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 23 suka samu raunuka daban-daban a lokacin da wata mota dauke da shanu da fasinjoji ta yi hatsari a kusa da kofar Foursquare Camp da ke kan hanyar Legas zuwa Ibadan a jiya Litinin.

Mai magana da yawun hukumar kiyaye hadurra ta jihar Ogun, Afolabi Odunsi, ya sanar da cewa hatsarin ya afku ne da misalin karfe 12 na rana.

A cewar Odunsi, hatsarin ya afku ne a sakamakon gudun wuce kima wanda ya haifar da kwacewar tuki.

Ya kara da cewa mutane 29 ne suka samu hatsarin, inda 23 suka samu raunuka, shida kuma suka rasa rayukansu.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: