Amurka da Iran na Shirin Fara Muhimman Tattaunawar Sulhu a babban birnin ƙasar Fakistan, Islamabad.

Amurka da Iran na Shirin Fara Muhimman Tattaunawar Sulhu a babban birnin ƙasar Fakistan, Islamabad.

Amurka da Iran na shirin fara muhimman tattaunawar sulhu a birnin Islamabad na ƙasar Fakistan, domin ƙarfafa tsagaita bude wuta bayan makonni na rikici mai tsanani a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ana sa ran manyan jami’ai za su jagoranci bangarorin biyu. 
A bangaren Amurka akwai mataimakin shugaban ƙasa JD Vance tare da wakilai na musamman Steve Witkoff da Jared Kushner. A bangaren Iran kuwa akwai ministan harkokin waje Abbas Araghchi da kakakin majalisar dokoki Mohammad Bagher Ghalibaf.

Tattaunawar na zuwa ne bayan tsagaita wuta na makonni biyu da aka cimma ta hannun Pakistan, bayan yaƙin makonni shida wanda ya girgiza kasuwannin mai na duniya tare da ƙara tashin hankali a yankin.

Manyan Batutuwan Tattaunawa:

Shirin nukiliyar Iran

Buɗe mashigar Strait of Hormuz

Sassauta takunkumin tattalin arziki kan Iran

Rikice-rikicen yankin, musamman a Lebanon.

Amurka na son Iran ta takaita shirinta na nukiliya da makamai masu linzami, tare da bude hanyoyin jigilar mai. 
Ita kuma Iran na neman a dage takunkumi, a saki kadarorinta da aka kulle, tare da amincewa da rawar da take takawa a yankin.

Sabani Mai Tsanani:
Duk da shirin tattaunawar, akwai manyan sabani:

Iran na bukatar a tsagaita bude wuta a Lebanon

Yayin da Amurka ta ki haɗa batun Lebanon a cikin yarjejeniyar.

Har yanzu ana takaddama kan ikon mashigar Hormuz

Wadannan sabani na jefa shakku kan yiwuwar samun nasarar tattaunawar.

Haka zalika Matsin Lamba na Ƙaruwa,
Inda Shugaban Amurka Donald Trump ya yi gargadin cewa za a iya komawa amfani da karfin soja idan tattaunawar ta ci tura, yayin da Iran ke ci gaba da matsa lamba ta hanyar takaita zirga-zirgar jiragen ruwa.

Ana kallon wannan tattaunawa a matsayin muhimmin mataki: ko dai ta kawo zaman lafiya mai ɗorewa, ko kuma ta sake haddasa sabon rikici a yankin.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: