Jam'iyyar APC mai mulki tace kofarta a bude take idan Kwankwaso na son komawa cikinta.


Jam'iyyar APC mai mulki tace kofarta a bude take idan Kwankwaso na son komawa cikinta.

Shugaban jam’iyyar APC) na kasa, Nentawe Yilwatda, ya ce jam’iyya mai mulki a shirye take ta karbi tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Kwankwaso.

Yilwatda ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da ake samun sauye-sauye na siyasa da cece-kuce a siyasar jihar Kano, wanda kuma ya jawo martani daga Kwankwaso.

Idan za a tuna a kwanakin baya ne gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, ya sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC, tare da 'yan majalisar dokokin jihar da na wakilai.

Da yake magana a wata hira da aka yi da shi ranar Lahadi, shugaban jam’iyyar APC ya ce duk da cewa jam’iyyar ba ta tattauna da tsohon gwamnan Kano a halin yanzu ba, amma idan ya zabi komawa jam’iyyar APC zai samu kyakkyawar tarba.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: