Tsohon ministan shari'ar Najeriya, Abubakar Malami ya bukaci kotu tayi watsi da umurnin kwace mashi kadarorin sa da hukumar EFCC ta yi na wucin gadi

Tsohon ministan shari'ar Najeriya, Abubakar Malami ya bukaci kotu tayi watsi da umurnin kwace mashi kadarorin sa da hukumar EFCC ta yi na wucin gadi

Tsohon ministan shari'ar Najeriya, Abubakar Malami ya bukaci kotu tayi watsi da umurnin kwace mashi kadarorin sa da hukumar EFCC ta yi na wucin gadi.

Tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, ya bukaci babbar kotun tarayya da ke Abuja da ta yi watsi da umarnin wucin gadi na kwace wasu kadarorinsa ga gwamnatin tarayya ta yi, inda ya dage cewa an mallaki dukiyar sa bisa gaskiya kuma an bayyana shi gaba daya ga hukumomi.

A ranar 6 ga watan Janairu mai shari’a Emeka Nwite ya bayar da umarnin kwace wasu kadarori 57 na wucin gadi ga Malami da ‘ya’yansa biyu, Abdulaziz da Abiru Rahman, biyo bayan wani tsohon takardar da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa ta gabatar.

Alkalin kotun ya bayyana cewa, ana zargin kadarorin an same su ne ta haramtacciyar hanya, sannan ya umarci EFCC ta kwace su na wani dan lokaci.

Sai dai Malami, ta bakin lauyansa, Joseph Daudu (SAN), a wata takarda da ya gabatar a ranar Litinin, ya zargi hukumar EFCC da bin umarnin wucin gadi ta hanyar danne ainihin bayanai da kuma bata suna.

Tsohon AGF ya bukaci kotun da ta yi watsi da karar da aka shigar, yana mai gargadi kan abin da ya bayyana a matsayin "sakamako masu cin karo da juna," yayin da ya ce matakin ya keta hakkinsa na mallakar dukiyarsa da tunaninsa da  lafiyarsa da rayuwar iyalinsa.

A cikin takardar bukatar mai lamba FHC/ABJ/CS/20/2026 da aka shigar a ranar 27 ga watan Janairu, Malami ya kalubalanci kwace wasu kadarorinsa uku da aka jera a lamba 9, 18, da 48 a takardar EFCC.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: