Iran ta kama wasu 'yan kasashen waje su 139 wadanda ke da hannu a zanga-zangar tsadar rayuwa na baya-bayan nan a ƙasar.

Hukumomin Iran sun kama wasu 'yan kasashen waje 139 a kasar wadanda ta zarga da hannu a lokacin zanga-zangar kin jinin gwamnati a baya-bayan nan, kamar yadda kafafen yada labaran ƙasar suka ruwaito yau Talata.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na Iran ya ruwaito babban jami'in 'yan sanda a birnin Yazd na cewa wadanda aka kama suna da hannu wajen shirya tarzoma da kuma jagorantar ayyukan tarzoma a Lokacin zanga-zangar, kuma a wasu lokuta suna hulda da cibiyoyin sadarwa a wajen kasar.

Ba a fayyace asalin kasashen wadanda aka kama ba zuwa yanzu.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: