Kungiyar kwallon kafar Super eagles ta rasa damar wakiltar Najeriya a gasar cin kofin kwallon kafa na Duniya Wanda za'a buga badi a Kasashen Amurka da Kanada da Mexico bayan ta yi rashin nasara a hannun DR Congo a wasan karshe na cike gurbin gasar ta Duniya.
Ta yi rashin nasaran ne a bugun fanareti bayan da aka tashi wasan 1-1.
Yayin da 'yan wasan Najeriya suka barar da bugu uku na DR Congo suka barar da bugu biyu.
Wannan Nasara da DR Congo din ta samu ya bata daman wakiltan nahiyar African a wasannin cike gurbin gasar ta Duniya da za'a fafata a Kasar Mexico a watan Maris na badi 2026.

0 Comments:
Post a Comment