Karamin Ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle ya isa birnin Kebbi

Karamin Ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle ya isa birnin Kebbi

Karamin Ministan Tsaron Najeriya, Bello Mohammed Matawalle, ya isa Birnin Kebbi bisa umarnin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na gaggauta komawa jihar don taimakawa wajen ceto ‘yan matan da aka sace a makarantar Sakandare ta ’yan mata ta Gwamnati, a garin Maga dake karamar hukumar wasagu.

Bayan isowar Ministan, kai tsaye ya shiga wata ganawar sirri da manyan hafsoshin tsaron jihar da suka hada da manyan hafsoshin Soji, da kwamandojin ‘yan sanda, da shugabannin sauran hukumomin tsaro.

Taron wanda aka gudanar a Birnin Kebbi, yana da nufin duba bayanan sirri, da karfafa hadin kai, da kuma hanzarta ayyukan bincike da ceto da aka fara gudanarwa.

Duk da cewa Matawalle bai yi wa ‘yan jarida jawabi ba kafin shiga wurin taron, jami’an tsaro da ke da masaniya kan ajandar taron sun ce zaman zai mayar da hankali ne wajen tsaurara tsare-tsaren gudanar da aiki da kuma rufe gibin da aka gano.

Wani babban jami’in tsaro, wanda ya bukaci a sakaya sunansa saboda ba shi da izinin yin magana da manema labarai, ya ce, “ Zuwan Ministan yana nufin ayyukan sun shiga wani yanayi mai tsanani.

Umurnin daga Abuja a bayyane yake, dole ne a yi duk abin da ya dace don ganin an dawo da wadannan ‘yan matan cikin koshin lafiya.

Daga bisani gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yabawa Tinubu kan yadda ya tura manyan jami’an gwamnatin tarayya a kan lamarin.

A wata sanarwa da mai magana da yawun sa Ahmed Idris ya fitar, gwamnan ya ce gwamnatin jihar za ta bayar da duk wani tallafin da ya dace ga hukumomin tsaro.

“Mun yaba da martanin da gwamnatin tarayya ta yi cikin gaggawa.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: