Gwamnatin Jihar Katsina zata shirya mukabala tsakanin Sheikh Yahaya Masussuka da kwamitin malaman jihar.

Gwamnatin Jihar Katsina zata shirya mukabala tsakanin Sheikh Yahaya Masussuka da kwamitin malaman jihar.

Gwamnatin Jihar Katsina ta fitar da wata sanarwa a yau Talata inda ta bayyana cewa kwamitin malamai na Jihar zata shirya zama da Sheikh Yahaya masussuka domin ya kare kansa daga wasu tuhume-tuhume da ake zarginsa da su a lokutan gudanar da wa'azinsa.

A cikin takardar wacce ke dauke da sanyawar hannun Mai magana da yawun Sakataren gwamnatin Jihar Katsina, Ibrahim Aliyu Gafai, ta baiyana cewa "Gwamnatin katsaina ta samu korafe-korafe wanda ke bayyana cewa salon wa'azin Sheikh Yahaya masussuka ya sabawa koyarwar irin ta shari'ar musulunci, haka zalika ta samu wani korafin daga shehin malamin inda ya bayyana cewa Kungiyar Izalatul bid'a na cin zarafinsa da Kuma barazanar Kai mashi hari.

Hakanne yasa gwamnatin jihar Katsina ta tura da wadannan korafe-korafen zuwa majalisar sarakunar kasar dake karkaahin jagorancin Mai martaba sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman CFR.
Inda sarkin ya gaiyaci dukkan bangarorin biyu fadarsa, ya Kuma tattauna da kowannesu tare da yanke matsayar cewa ba'a yarda kowane bangare ya gudanar da wa'azin da zai ci zarafin wani ba.

Sai dai gwamnatin Katsina tace lamarin ya cigaba duk da zaman da akayi a fadar sarkin na Katsina, Wanda hakanne yasa gwamnatin ta shirya mukabala tsakanin Sheikh Yahaya masussuka da kwamitin malamai na jihar domin ya zo ya kare kansa daga zargin da akeyi masa. 

Gwamnatin ta Katsina ta ce bayan kammala zaman jin bayani da kwamitin, za a kirkiro sabbin ka’idojin wa'azi a fadin jihar, domin tabbatar da tsari da guje wa rigingimu tsakanin malamai.

Sanarwar ta kuma ce gwamnati za ta hukunta duk wanda ya karya ƙa'idojin da za a cimma, domin tabbatar da zaman lafiya da daidaito tsakanin masu wa’azi a jihar.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: