Dan wasan na Morocco wanda ke taka leda a Kungiyar kwallon kafar PSG ta Faransa ya samu wannan nasaran ce bayan ya doke abokan takaransa Mohamed Salah na Egypt da Victor Osimhen na Najeriya.
Wannan shine Karan farko da wani mai tsaron baya ya lashe gasar a cikin Shekaru 52, tun bayan dan wasan Zaire, Bwanga Tshimen da ya lashe kyautar a Shekarun 1973.
Haka zalika wannan ne karo na biyu da dan wasan Morocco ke lashen kyautar a tarihi baya ga Mustapha Hadji da ya lashe kyautar a Shekarun 1998.
Da yake jawabi a lokacin karfar kyautar Dan wasan na Morocco da Kungiyar PSG yace:
"Wannan lambar yabo tana da matukar kima a gare ,"
"Tana wakiltar mafarkin yawancin matasan Afirka waɗanda suke da mafarkin cimma burinsu na kaiwa matsayi mafi girma.
Don haka ina sadaukar da wannan nasaran tare da duk wanda ya tallafa mini tun ina ƙarami."
Haka zalika a bangaren Mata Yar wasan gaba Ghizlane Chebbak ta samu kyautar Gwarzon ‘Yan wasan Mata, yayin da mai tsaron ragar tawagar ‘yan wasan kasar Morocco, Yassine Bounou, wadda a halin yanzu ke taka leda a kungiyar Al-Hilal, ya samu kyautar Gwarzon mai tsaron ragar ta bana.

0 Comments:
Post a Comment