Yadda Wani bawan Allah ya ba mai talla akan titi kyautar N50,000

Yadda Wani bawan Allah ya ba mai talla akan titi kyautar N50,000

Allah Sarki, A cikin wannan bidiyon dake kasa zaku ga yadda Wani bawan Allah ya ba wani mutum mai fama da laluran kafafu amma duk da haka yake neman na kanshi akan titi kyautar Naira dubu N50,000. 
Inda nan take ya tura mashi ta asusun banki shi.

Bisa alamu ya tausaya ma shi ne saboda yadda ya ganshi Yana fama da laluran rashin lafiyan kafafunsa Amma duk da haka bai tsaya yayi roko ko bara ba inda ya dauki kayan sana'ar shi yana yin talla akan titi.

Bayan ya tura mashi N50,000 din ta asusun bankinsa, Mai suna Yakubu Isa ta bankin Access Bank, ya Kuma umurce shi da ya tafi gida ya huta saboda kafafunsa dake da lalura.

Allah madaukakin sarki ya bamu ire-iren wadannan nutanen a cikin Al'umma.




SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: