Kamar yadda Alkaluma suka nuna a shafin babban bankin Najeriya CBN Darajan Naira ya karu idan aka kwatanta da yadda aka chanja ta akan Dallar Amurka a kwanakin baya.
Ranar Juma'a an canja Dalar Amurka daya akan N1,480.66 idan aka kwatanta da yadda aka sayar da ita N1,488.26 a ranar Alhamis, wanda hakan ke nuna cewa an samu raguwar N7.6 a farashin na Babban bankin Najeriya, CBN.
Sai kasuwar bayan fage inda aka sayar da Dalar Amurka daya akan
N1,495 a ranar Juma'a idan aka kwatanta da yadda aka sayar da ita akan N1,497 inda aka samu ragin N27 a kasuwar ta bayan fage.

0 Comments:
Post a Comment