Talauci da rashin wayar da kan iyaye shi ke hana yara zuwan Makaranta a Sokoto

Talauci da rashin wayar da kan iyaye shi ke hana yara zuwan Makaranta a Sokoto

Shugabannin al’umma a jihar Sokoto sun bayyana talauci da rashin wayar da kan iyaye a matsayin manyan matsalolin da jihar ke fama da ita game da yawaitan yara da ba su zuwa makaranta.

Sun nuna damuwar ne a yayin ziyarar da wakiliyar asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, Ms Wafa Said, ta kai makarantar firamare ta SKS Model Primary School da ke Yabo, inda masu ruwa da tsakin suka sabunta kudurin su na tunkarar kalubalen.

Da yake jawabi, shugaban al’ummar Yabo, Muhammadu Abubakar, ya baiyana cewa, talauci da rashin sanin ya kamata su ne ke hana yara zuwa makaranta.

Ya ce, "A koyaushe muna wa'azi game da ilimi a lokacin wa'azi, na tabbatar da cewa dukan 'ya'yana sun sami ilimin jami'a, wasu har zuwa matakin digiri. Mun yi imani da ilimi sosai."

Duk da haka, maahalarta taron sun ce magance talauci da zurfafa wayar da kan iyaye yana da matukar muhimmanci wajen sauya salon rashin zuwan yara makaranta a Sakkwato.

Da take jawabi, wakiliyar UNICEF a Najeriya, Misis Wafa Said, wacce ta nuna damuwa cewa yara da yawa har yanzu suna yawo a kan tituna maimakon zama a cikin azuzuwa, ta kuma jaddada cewa ilimi ya kasance shi ke samar da sauyi a cikin al'umma.

"Lokacin da aka bai wa yara damar samun ilimi, ba wai kawai an canza al'ummominsu ba ne, za kuma su kasance masu bayar da gudummawa ga Afirka da ma duniya baki daya,"  ta kuma da ci gaba da hadin gwiwa tsakanin hukumomin makarantu da masu ruwa da tsaki a cikin al'umma.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: