Hukumar kula da jin dadin alhazai ta kasa NAHCON ta fitar da jadawalin farashin maniyyata aikin hajjin shekaran 1447/2026 a hukumance, inda farashin ya kama daga naira miliyan 8.1 zuwa miliyan 8.5, gwargwadon wurin da mahajjatan zasu tashi.
Shugaban Hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ne ya sanar da hakan, bayan kulla wasu muhimman yarjejeniyoyin hidima da abokan huldar a kasar Saudiyya domin gudanae da aikin hajji mai zuwa.
Sanarwar da sashen yada labarai ya fitar ta ce: “Bayan tuntubar juna da dukkan masu ruwa da tsaki da suka hada da kungiyar shugabannin kasashe da kuma samun amincewar gwamnatin tarayya, Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya, Farfesa Abdullahi Sale Usman ya sanar da kudin aikin Hajjin shekaran 2026 kamar haka:
Yankin Maiduguri-Yola
(Yobe, Borno, Adamawa da Taraba) za su biya -N8,3.18
Jihohin Arewa. N8,244,813.67
yayin da Jihohin Kudu za su biya Naira 8,561,013.67 idan aka kwatanta da abin da aka biya a shekarar da ta gabata, kowane maniyyaci zai samu saukin Naira 200,000.”

0 Comments:
Post a Comment