Akalla mutane 36 ne suka mutu, sama da 50 suka jikkata a wani gangamin da tauraron fina-finan Indiya Vijay thalapathy ya gudanar.
Akalla mutane 36 ne suka mutu yayin da fiye da 50 suka jikkata a ranar Asabar a wani gangamin da dan wasan kwaikwayon fina-finan Indiya na Tamil Vijay thalapathy, wanda ke yakin neman zabe a matakin jiha ya yi.
Babban Ministan Tamil Nadu MK Stalin ya ce yara takwas da mata 16 na daga cikin mutane 36 da suka mutu a gundumar Karur a Tamil Nadu yayin wani gangamin siyasa da Tamilaga Vettri Kazhagam, jam'iyyar Vijay ta gudanar.
Jama'a da dama ne suka taru domin taron wani bangare na ziyarar da Vijay ke ci gaba da yi wa jam'iyyarsa ta siyasa, Tamilaga Vettri Kazhagam.

0 Comments:
Post a Comment