A wani rahoto da mujallar Forbes wacce ke kididdiga kan harkokin kudade a duniya ta fitar, ta aiyana kudin Najeriya a matsayin na 9 a jerin kudaden Afrika da basu da daraja akan Dalar Amurka.
A bayanin kididdigar ta mujallar Forbes din ta fitar a wannan watan, kudin kasar São Tomé & Príncipe Dobra shine kudin da yafi kowanne rashin daraja a Afrika inda ake chanja shi akan (22,282 ga Dalar Amurka $1).
Sannan sai kudin kasar Sierra Leonean Leone akan (20,970), sai na kasar Guinean Franc (8,680),
Ugandan Shilling (3,503), sai na kasa Burundian Franc (2,968).
Sauran sune kudin kasar Kongo, Congolese Franc (2,811), sai
Tanzanian Shilling (2,465), sai kudin kasar Malawi, Malawian Kwacha (1,737), sannan sai kudin Najeriya, Naira (₦1,490 per $1), sai kudin Ruwanda a mataki na 10, Rwandan Franc (1,448).

0 Comments:
Post a Comment