Champions League: Liverpool zata ziyarci Galatasary na kasar Turkiya
Kungiyar kwallon kafar Liverpool zata ziyarci Galatasary na kasar Turkiya domin kece raini a wasan Zakarun turai na Champions League a yau Talata da misalin karfe 8:00pm agogon Najeriya.
A wasan farko da Galatasaray ta buga tasha kashi ne a hannun Kungiyar kwallon kafar Eintracht Frankfurt dake Jamus da ci 5-1 Yayin da Liverpool ta doke Athletico Madrid da ci 3-2 a filin wasa na Anfield.
Galatasary ce ke jan ragamar teburin gasar Super Lig na Turkiya bayan da ta samu nasara a duka wasanni 7 bakwai da ta buga, Yayin da ita ma Liverpool din ta lashe wasanni 6 daga cikin 7 da ta buga a wasan Premier League na bana Wanda hakan ya bata daman jan ragamar teburin na premier league.

0 Comments:
Post a Comment