A yau Talata 30 ga watan satumba 2025 dagajan naira ya karu idan aka kwatanta shi da yadda aka canja dalar Amurka a makon da ya gabata akan N1510 akan kowace dalar Amurka daya, hakan na nufin an samu ragowar N10 kenan akan kowace dala $1.
Sai dai farashin gwamnati Wanda Babban bankin Najeriya CBN ke fitarwa, darajan Nairan raguwa yayi da kobo 15, saboda a yau Talata ana canja dalar Amurka daya $1 akan Naira N1480.15 maimakon N1480 da aka canja a makon jiya.
Haka zalika tazaran farashin gwamnati da kasuwannin bayan fage ya ragu daga N30 a makon jiya zuwa N19.85 a wannan makon.
Idan dai baa manta ba a wannan makon mujallar Forbes wacce ke kididdiga kan harkokin kudade a duniya ta aiyana kudin Najeriya a mataki na 9 a jerin kudaden Afrika 10 da basu da daraja akan dalar Amurka.

0 Comments:
Post a Comment