Kungiyar kwallon kafar Manchester United zata kece raini da Athletico bilibao na kasar sifaniya a gasar cin kofin Europa League matakin dab da na karshe a Filin wasa na old traford dake birnin Manchester na Kasar ingila.
A wasan da Suka fafata a zagayen farko a ranar alhamis da ta gabata, Manchester United ce ta samu nasara akan Bilbaon da ci 3-0, Dan wasan tsakiyar United Casemero ne ya fara bude raga a mintuna 30 da fara wasan.
Sai dai Dan wasan Bilbaon D.Vivian ya samu Jan Kati a lokacin da ya janyo Dan wasan gaban United Hojlund a da'iran bugun fanareti, Wanda sakamakon haka aka ba United din bugun fanareti Inda Kaftin din kungiyar Bruno Fernandez ya zura kwallon ta biyu a ragar Bilbaon Kafin daga bisani ya Kara zura kwallo ta uku a mintuna 45.
Masana harkan wasanni na ganin cewa Manchester United ta zura kafar ta daya a matakin zuwa wasan karshe Inda zata yi fatan fafatawa da daya daga cikin Tottenham Hotspur ko Bordo/Glimt idan ta samu nasaran doke Bilbaon.
Masu iya magana dai na cewa ba'a San maci tuwo ba sai Miya ta kare.
0 Comments:
Post a Comment