Kungiyar kwallon kafar Inter Milan ta Kai wasan karshe na UEFA Champions League

Kungiyar kwallon kafar Inter Milan ta Kai wasan karshe na UEFA Champions League

Kungiyar kwallon kafar Inter Milan na kasar italiya ta samu nasaran kaiwa zagayen wasan karshe na cin kofin zakarun turai UEFA Champions League bayan ta doke Barcelona na ci 4-3 a Filin wasa na sansiro.

Wasan yaja hankalin Yan kallo a fadi duniya duba da yadda aka fafata a zagayen farko a Filin wasa na Camp nou dake birnin Barcelona na kasar sifaniya inda aka tashi wasan 3-3.

Sai dai a wannan wasan zagaye na biyu shima an fafata bayan da Inter Milan din ta fara zura kwallaye har biyu a ragar Barcelona ta hannun Dan wasan gabanta Lautaro Martinez.
Sai dai Barcelona nan tayi bajinta Inda ta farke kwallayen bayan an dawo hutun Rabin lokaci ta hannun 'yan wasanta Eric Garcia da Dani Olmo sannan Barcelonan ta kara kwallo ta uku a ragar Inter Milan din a mintuna 85 ta hannun Raphinha Inda jimullan kwallayen kungiyoyin ya zama 6-5.

Ana saura minti daya kacal a tashi wasan ne inter Milan ta farke kwallon ta hannun Dan wasanta F.Acerbi Inda aka tashi wasan wasan 3-3 wato 6-6 kenan jimullan kwallayen kungiyoyin lamarin da ya sa aka kara mintuna 30.

Sai dai a mintuna na 99 da Karin lokaci Inter Milan ta zura kwallo ta 4 a wasan ta hannun dan wasanta D.Frattesi Inda aka tashi wasan 4-3 (7-6 jimulla) Wanda hakan yaba Inter Milan din nasaran zuwa wasan karshe na cin kofin zakarun turai na wannan shekaran Inda zasu fafata a tsakanin Arsenal ko PSG wadanda zasu buga wasansu ranar Laraba da 8pm.





SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: