Jirgin kasa mafi gudu a duniya

Jirgin kasa mafi gudu a duniya

Hakika a kullum cigaban zamani a fannin kere-kere na cigaba da kawo sauye-sauye da rayuwa mai sauki a fannonin daban-daban na rayuwar dan Adam.

A fannin sufuri an Samu cigaban dake saukaka zirga-zirga cikin hanzari a dan kankanin lokaci Wanda idan ba Wanda ya sani ba sai mutum Yace karya ne hakan ba zaiyiwu ba.

Sanin kowane a kasashe irin namu dake nahiyar afrika, idan ana maganar abun sufuri mafi sauri baya ga jirgin sama Babu abun dake zuwa zuciyoyin Mutane sai mota.

To a Halin yanzu zancen ba haka yake ba musamman a kasashen da Suka riga Suka cigaba irin su China, Japan, France, England da USA.

Jirgin kasa a irin wadannan kasashen ya kasance abun sufuri mafi sauri Wanda zai kaika Inda zaka je cikin sauri a lokaci kankani.

Mutane zasu yi mamaki kasancewa mu a nahiyar mu ta Afrika idan akayi maganan jirgin kasa to Babu abin da zai zo zukatan Mutane illa irin yadda yake daukar tsawon lokaci bai Isa Inda zashi ba.

Saboda haka dalilin wannan bayanin shine domin mu sanar maku cewa duniya ta rigaya ta cigaba illa kawai mune aka barmu a baya.

A cikin wannan mukalar zamu kawo maku jerin jiragen kasa mafiya sauri (gudu) a duniya, wata Kila Mai sauraro Yace "karyane" to ba karyatawa akeyi ba bincikawa Ake yi domin tabbatar da gaskiyar maganar.

Jirgin kasar da yafi kowane gudu a duniya shine Shanghai Maglev dake kasar China Wanda zai iya gudun kilo Mita 460 a cikin sa'a daya, ma'ana zai iya tashi daga Kano zuwa Lagos a cikin Sa'a 2.3.
Wato Wannan jirgin zai iya gudun kilo Mita 7 a cikin minti daya kacal.


Amma izuwa yanzu gudun da jirgin ya taba yi shine tafiyan kilo Mita 501 a cikin sa'a daya Wanda yayi ta daga tashan jirgin kasar Longyang a birnin Shanghai na China zuwa tashan Filin jirgin sama dake Pudong a Shanghai din.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: