’Yan Sanda Sun Tarwatsa Wata Masana’antar Sayar da Jarirai a jihar Ogun, Inda Suka Ceto Mata Masu Juna Biyu da Yara ƙanana.

’Yan Sanda Sun Tarwatsa Wata Masana’antar Sayar da Jarirai a jihar Ogun, Inda Suka Ceto Mata Masu Juna Biyu da Yara ƙanana.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun ta tarwatsa wata cibiyar da ake zargin ana gudanar da sayar da jarirai da fataucin mutane a yankin Mowe na jihar, inda ta ceto mata biyu masu juna biyu da yara huɗu, tare da kama mutane shida.

’Yan sandan sun ce an gudanar da samamen ne a ranar Litinin, 24 ga Agusta 2026, a layin Toluwalase dake ƙauyen Abaren, Mowe, bayan samun bayanan sirri kan zargin fataucin mutane da kuma tallata yara ba bisa ƙa’ida ba.

Matan da aka ceto sun haɗa da Ilesanmi Foluke mai shekaru 23, wadda ke da cikin wata bakwai, da Ejekwa Melody mai shekaru 20, wadda ke da cikin wata takwas. Yaran da aka ceto sun kasance maza biyu da mata biyu.

’Yan sandan sun ce waɗanda aka kama sun haɗa da mutane biyar da kuma wata ma’aikaciyar jinya da ake zargi da hannu a lamarin.

Binciken ’yan sanda ya kuma kai su wani asibiti a yankin Mowe, inda suka gano wata Blessing Bright Effiong, mai shekaru 26, wadda ta haihu da ɗa namiji a ranar 20 ga Agusta. Sai dai ba a iya gano inda jaririn yake ba, lamarin da ya sa aka kama ma’aikaciyar jinyar domin taimakawa wajen gano jaririn.

An tura lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID), Eleweran, Abeokuta, domin ci gaba da bincike.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ogun, Bode Ojajuni, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin, tare da kira ga jama’a da su kasance masu taka-tsantsan tare da kai rahoton duk wani abin da suke zargi ga jami’an tsaro.

Lamarin ya zo ne bayan da a baya aka gano wata cibiyar da ake zargin Masana’antar Sayar da Jarirai ne a jihar Lagos, inda aka ceto mata 18 masu juna biyu da yara 10.

0 $type={blogger}: