Tinubu ya yaba wa Hausawa, Inda Ya cee su ginshiƙai ne masu muhimmanci ga haɗin kan Najeriya

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana al’ummar Hausawa a matsayin “manyan ginshiƙai” da ke taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da haɗin kai da ci gaban Najeriya.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana al’ummar Hausawa a matsayin “manyan ginshiƙai” da ke taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da haɗin kai da ci gaban Najeriya.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 26 ga Agusta, 2026, a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X domin taya al’ummar Hausawa murnar Ranar Hausa, wadda ake gudanar da bukukuwanta a fadar Daura mai tarihi da ke Jihar Katsina.

Shugaban ya ce harshen Hausa ya bunƙasa sosai, inda ya zama ɗaya daga cikin muhimman harsunan haɗin kai da kasuwanci a duniya.

Tinubu ya ce:
> “Al’ummar Hausawa manyan ginshiƙai ne waɗanda ke taka muhimmiyar rawa wajen haɗin kan Najeriya da ci gabanta.”

Ya kuma taya al’ummar Hausawa da ke faɗin duniya murnar wannan rana, yana mai jaddada muhimmancin harshen Hausa da al’adun Hausawa.

Ranar Hausa, wadda kuma ake kira Ranar Hausa ta Duniya ko Ranar Hausa, ana bikin ta ne duk shekara a ranar 26 ga Agusta.

An fara bikin ne a matsayin wani shiri na kafafen sada zumunta da ɗan jaridar Najeriya Abdulbaki Aliyu Jari ya ƙaddamar domin bunƙasa amfani da harshen Hausa a intanet tare da wayar da kan jama’a game da muhimmancin al’adun Hausa.

Daga bisani bikin ya yaɗu zuwa ƙasashe daban-daban a Afirka, Turai, Gabas ta Tsakiya, Asiya da Amurka.

Harshen Hausa na daga cikin manyan harsunan Najeriya, kuma yana cikin harsunan da aka fi amfani da su a Afirka, inda miliyoyin mutane ke magana da shi a sassa daban-daban na duniya.

0 $type={blogger}: