Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Accord yayi alkawarin dawo da farashin man fetur ₦605 Idan aka zabe shi a 2027.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Accord yayi alkawarin dawo da farashin man fetur ₦605 Idan aka zabe shi a 2027.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Accord, Dr Gbenga Olawepo-Hashim, ya ce idan aka zaɓi jam’iyyarsa a zaɓen 2027, zai rage farashin litar fetur zuwa ₦605.

Olawepo-Hashim, wanda ya dade yana adawa da cire tallafin man fetur, ya ce farashin ₦605 ba zai zama tallafi na bogi ba. 
Ya ƙara da cewa za a iya cimma hakan ba tare da rage kuɗaɗen shiga na gwamnati ko rabon kuɗaɗen FAAC ba.

Ya ce ya kamata a mayar da hankali wajen gano ainihin kuɗin da ake kashewa wajen hako ɗanyen mai, tace shi, jigilar sa da rarraba fetur, maimakon ɗaura farashin cikin gida kai tsaye da farashin kasuwar duniya.

Dan takarar ya kuma yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa kan tsarin man fetur na ƙasar, domin gano ainihin kuɗin samarwa da kuma sauran kuɗaɗen da ake kashewa a sarkar man fetur.

Ya ce binciken ya kamata ya shafi hako ɗanyen mai, kwangiloli, sayayya, matatun mai, sufuri, ajiya, inshora, bututun mai da rarraba fetur.

Olawepo-Hashim ya kuma ce gwamnatin Accord za ta yi kokarin daidaita canjin kuɗi tsakanin ₦525 zuwa ₦700 kan dala ɗaya, yana mai cewa hakan zai rage tsadar kayan da ake amfani da su a masana’antar man fetur.

Ya yi alkawarin ƙara saurin tace man fetur a cikin gida, inganta gaskiya a harkar man fetur da kuma rage almubazzaranci da asarar kuɗaɗe.

Sai dai ya bayyana cewa hasashen farashin fetur na ₦200 zuwa ₦300 ba alkawari ba ne na gaggawa, illa dai sakamakon da ake sa ran samu nan gaba idan aka rage kuɗin samar da man fetur tare da samun daidaiton darajar naira.

Ya ce burinsa ba wai kawai samar da fetur mai arha ba ne, illa gina tattalin arzikin Najeriya mai inganci, inda makamashi mai sauƙin farashi zai taimaka wajen rage kuɗin sufuri da masana’antu, ƙara ƙarfin sayen jama’a da kuma bunƙasa kuɗaɗen shiga na gwamnati.

0 $type={blogger}: