Shahararren Mawaƙin Siyasa, Kosan Waka, Ya Rasu Yana da Shekaru 47.

Shahararren Mawaƙin Siyasa, Kosan Waka, Ya Rasu Yana da Shekaru 47.

Shahararren mawaƙin siyasa, Muhammadu Buhari, wanda aka fi sani da Kosan Waka, ya rasu ranar Lahadi yana da shekaru 47.

Marigayin ya shahara wajen rera waƙoƙin siyasa, musamman waɗanda ke goyon bayan Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

A cikin saƙon ta'aziyyar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana rasuwar Kosan Waka a matsayin babban rashi ga masana'antar nishaɗi da kuma al'umma baki ɗaya.

Ya ce marigayin ɗan asalin Jihar Katsina ne mai kishin ƙasa, wanda waƙoƙinsa suka taka muhimmiyar rawa wajen sadarwar siyasa da bunƙasa al'adun Hausa da wayar da kan jama'a a Kano da sauran sassan Najeriya.

Sanarwar ta ce an yi jana'izar marigayin da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin ranar Lahadi a garinsu na Tsanni da ke Ƙaramar Hukumar Batagarawa a Jihar Katsina.

Gwamnan ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin, musamman mahaifiyarsa, da abokansa da masoyansa da al'ummar Jihar Kano.

Ya ƙara da cewa gudummawar da Kosan Waka ya bayar wajen haɓaka waƙoƙin siyasa da masana'antar nishaɗin Hausa za ta ci gaba da kasancewa abin tunawa.

Gwamna Yusuf ya kuma yi addu'ar Allah Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa, tare da bai wa iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi.

0 $type={blogger}: