Dan Sanda Da Fararen Hula Biyu ne Suka Mutu Yayin Harin Lakurawa a Kauyen Girkau na Jihar Sokoto.

Dan Sanda Da Fararen Hula Biyu ne Suka Mutu Yayin Harin Lakurawa a Kauyen Girkau na Jihar Sokoto.

Jami'in ɗan sanda daya da fararen hula biyu ne suka rasa rayukansu bayan wasu da ake zargin 'yan ta'addan Lakurawa ne suka kai hari kauyen Girkau da ke Ƙaramar Hukumar Kebbe a Jihar Sokoto.

Harin, wanda ya faru ranar Litinin, ya jikkata mutane da dama, yayin da maharan suka sace adadin shanu da ba a tantance ba tare da ƙone motocin tsaro guda biyu na Rundunar 'Yan Sandan Najeriya da kuma Hukumar Tsaron farin kaya ta Jihar Sokoto.

Kakakin Rundunar 'Yan Sandan Jihar Sokoto, Ahmed Rufai, ya tabbatar da cewa jami'an tsaro sun isa yankin bayan samun kiran gaggawa, inda suka fafata da maharan tare da tilasta musu tserewa. Sai dai jami'in ɗan sanda daya ya rasa ransa yayin musayar wuta.

Rundunar ta ce ta ƙara tsaurara matakan tsaro a yankin domin kare rayuka da dukiyoyin al'umma da kuma hana sake aukuwar irin wannan hari.

Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun kutsa cikin ƙauyen dauke da makamai masu yawa, inda suka riƙa harbe-harbe kan mai uwa da wabi, lamarin da ya sa mutane da dama suka tsere domin tsira da rayukansu.

Majiyoyin al'umma sun bayyana sunayen waɗanda suka mutu da suka haɗa da jami'in ɗan sanda Hussaini Manyu da wani dattijo mai suna Bala Wakili, da kuma wani matashin makiyayi da aka ce an kashe shi bayan ya ƙi mika shanunsa ga maharan.

Haka kuma, wani manomi ya samu raunin harbin bindiga yayin da yake aiki a gonarsa, kuma yana karɓar magani a asibiti. 
Wasu mazauna yankin sun kuma yi zargin cewa maharan sun ci zarafin wata matar aure bayan ta yi ƙoƙarin kare kanta daga yunkurin cin zarafi.

Shugabannin al'umma sun bayyana harin a matsayin ɗaya daga cikin mafi muni da yankin ya fuskanta a 'yan watannin nan, tare da yin kira ga Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Sokoto da su ƙara tura jami'an tsaro zuwa Kebbe da ƙananan hukumomin da ke makwabtaka domin dakile hare-haren da ake ci gaba da fuskanta.

0 $type={blogger}: