Dakarun Sojoji Sun Ceto Mutane 16 da Aka Sace, Tare da Kama Masu Taimaka wa 'Yan Ta'adda.

Dakarun Sojoji Sun Ceto Mutane 16 da Aka Sace, Tare da Kama Masu Taimaka wa 'Yan Ta'adda.

Dakarun Rundunar Sojin Najeriya sun ceto mutane 16 da aka yi garkuwa da su tare da kama wasu da ake zargi da taimaka wa 'yan ta'adda a wasu hare-haren tsaro da aka gudanar a jihohin Borno da Yobe da Sokoto da Zamfara da Filato.

Rahoton rundunar ya bayyana cewa, a cikin awanni 24 da suka gabata, sojojin sun kuma kwato dabbobi 281 da aka sace da babura biyu da wayoyin hannu da wasu miyagun ƙwayoyi da ake zargi da kuɗaɗe da sauran kayayyakin da ake kyautata zaton suna da alaƙa da ayyukan ta'addanci.

A Jihar Borno, sojojin sun cafke mutum 20 da ake zargin 'yan mayaƙan Boko Haram ne, ciki har da mata da maza da yara, bayan sun tsere daga sansanin 'yan ta'adda sakamakon rikici tsakanin Boko Haram da mayaƙan ISWAP.

Haka kuma, an kama wasu da ake zargi da kai wa 'yan ta'adda kayan tallafi da miyagun ƙwayoyi a jihohin Yobe da Borno. 
Daga cikin kayayyakin da aka ƙwato akwai tabar wiwi da ake zargi da wayoyin hannu da kuɗaɗe da wuƙar hari da katin shiga sansanin ISWAP.

Sojojin sun kuma ceto wata mata da aka yi garkuwa da ita tun watan Nuwamban 2025, inda aka ba ta kulawar lafiya kafin a haɗa ta da iyalanta.

A yankin Arewa maso Yamma, dakarun Operation FANSAN YAMMA sun ceto mutane 14 da aka sace a Jihar Sokoto, tare da kwato dabbobi 281 da aka sace da babura biyu bayan fafatawa da 'yan ta'adda.

A wasu hare-hare daban a jihohin Sokoto da Zamfara, 'yan bindiga sun tsere sun bar wasu mutum biyu da suka yi garkuwa da su, ɗaya daga cikinsu na ɗauke da raunin harbin bindiga, inda aka garzaya da shi asibiti domin samun kulawar likitoci.

A Jihar Filato kuwa, sojoji sun ceto manoma da suka jikkata bayan harin da ake zargin makiyaya masu ɗauke da makamai ne suka kai musu. Sun kuma kwato shanu 27 daga hannun maharan tare da kama mutane 19 a wani samame da aka kai bayan kashe sojoji biyu a wani kwanton ɓauna.

Rundunar Sojin Najeriya ta ce za ta ci gaba da gudanar da irin waɗannan hare-haren domin murƙushe 'yan ta'adda, ceto waɗanda aka sace, da kuma tabbatar da zaman lafiya a sassan ƙasar da matsalar tsaro ta shafa.

0 $type={blogger}: