An Kama Mutane Biyar Kan Zargin Sayar da Naman Shanun da Suka Mutu a Jihar Borno

An Kama Mutane Biyar Kan Zargin Sayar da Naman Shanun da Suka Mutu a Jihar Borno

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Borno ta kama wasu mutane biyar bisa zargin yankawa da sayar da naman shanun da suka mutu ga jama'a ba tare da sun sani ba a birnin Maiduguri.

A cewar rundunar, an kama mutanen ne a ranar 29 ga watan Yuli bayan jami'an Rundunar Yaki da Manyan Laifuka (Crack Squad) sun samu sahihan bayanan sirri.

Kakakin rundunar, Nahum Daso, ya bayyana sunayen wadanda ake zargin da suka hada da Modu Umar mai shekaru 43 da Abba Mohammed mai shekaru 24 da Adam Abubakar mai shekaru 21da Faruq Gambo mai shekaru 19, da Mada Usman mai shekaru 24.

Binciken farko ya nuna cewa ana zargin mutanen da karbar shanun da suka mutu, sannan suka yanka gawarwakinsu tare da rarraba naman ga masu sayar da nama a gefen titi domin sayar wa jama'a.

Rundunar ta ce an kama su ne yayin da suke kokarin jigilar gawar wata matacciyar saniya zuwa yankin Morumti da ke Maiduguri domin ci gaba da sarrafawa da rabawa.

A halin yanzu, wadanda ake zargin suna tsare a hannun 'yan sanda yayin da ake ci gaba da bincike domin gano sauran masu hannu a lamarin da kuma hanyoyin da ake bi wajen rarraba naman. 
Bayan kammala bincike, za a gurfanar da su a gaban kotu.

Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Borno, Naziru Abdulmajid, ya bayyana cewa irin wannan aiki barazana ce ga lafiyar al'umma. 
Ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da hada kai da hukumomin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki domin dakile sayar da naman da bai dace da ci ba a fadin jihar.

Haka kuma ya sanar da cewa za a gudanar da taro da masu gudanar da mayanka da kungiyar mahauta da dillalan dabbobi da masu sayar da nama da hukumomin da ke kula da ingancin abinci domin kara tsaurara matakan sa ido da kare lafiyar jama'a.

Rundunar ta bukaci al'umma da su kasance masu taka-tsantsan tare da kai rahoton duk wani abin da ya shafi yankawa da sarrafawa da jigila ko sayar da nama da ake zargi ga ofishin 'yan sanda mafi kusa ko hukumomin da abin ya shafa.

0 $type={blogger}: