Ana fargabar mutane da dama sun makale bayan wata mummunar zaftarewar kasa da ta afku a gundumar Pengshui, da ke birnin Chongqing a kudu maso yammacin kasar Sin, inda ta kuma rushe gidajen zama da dama.
Rahotanni sun ce wani ma'aikacin al'umma ya fara lura da duwatsu suna fadowa da misalin karfe 8:00 na safe, lamarin da ya sa aka yi gaggawar gargadin mazauna yankin tare da fara kwashe sama da mutane 60 zuwa wuri mai aminci.
Sai dai kafin a kammala kwashe su, zaftarewar kasar ta faru da misalin karfe 9:08 na safe, inda ta binne wasu daga cikinsu.
Jami'an ceto sun samu nasarar ciro mutane tara daga karkashin baraguzan ginin, kuma an tabbatar da cewa babu wanda ke cikin mawuyacin hali. Har yanzu ba a tantance adadin mutanen da har yanzu suke makale ba.
Hotunan bidiyo daga wurin sun nuna yadda kasa da manyan duwatsu suka gangaro kan gidajen da ke bakin kogi, yayin da mazauna yankin ke gudun ceton rayukansu cikin gajimaren kura.
Ma'aikatar Kula da Gaggawa ta kasar Sin ta kaddamar da matakin gaggawa na biyu tare da tura tawagar masu ceto 100 zuwa yankin.
Haka kuma, an tura jami'an kashe gobara da masu aikin ceto 206 tare da motocin agaji 49 domin ci gaba da aikin ceto.
Har yanzu hukumomi ba su bayyana musabbabin zaftarewar kasar ba, yayin da ake ci gaba da neman wadanda ake zargin sun makale a karkashin baraguzan.

0 $type={blogger}:
Post a Comment