Ɗan tsohon Shugaban Ƙasar Najeriya, Goodluck Jonathan, mai suna Ariwera Jonathan, ya kammala karatunsa a Jami'ar Manchester Metropolitan da ke ƙasar Birtaniya.
Tsohon shugaban ƙasar ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook, inda ya taya ɗansa murnar kammala karatun tare da bayyana alfaharinsa da ƙoƙarin da ya yi wajen cimma wannan nasara.
Jonathan ya rubuta cewa:
> “Muna taya ɗanmu Ariwera murnar kammala karatunsa a Jami'ar Manchester Metropolitan. Ni da mahaifiyarka muna alfahari da ƙwazonka. Muna yi maka fatan alheri da samun kyakkyawar makoma a rayuwarka.”
Ya kuma wallafa hotunan bikin yaye ɗaliban da ya halarta tare da matarsa, Patience Jonathan, da ɗansu Ariwera.
Goodluck Jonathan da matarsa Patience suna da ’ya’ya biyu, Ariwera Jonathan da Aruabi Jonathan.
Iyalin sun bayyana wannan nasara a matsayin abin alfahari tare da yi wa Ariwera fatan samun nasara a rayuwarsa da aikinsa na gaba.

0 $type={blogger}:
Post a Comment