Akalla mutane 21, ciki har da yara 20 'yan makaranta da wani babban mutum daya, suka rayukansu bayan wata motar makaranta ta yi hatsari a gabashin ƙasar Uganda.
Motar na ɗauke da ɗaliban Makarantar King David Junior School da ke Kampala, waɗanda ke dawowa daga yawon buɗe ido zuwa Sipi Falls a gundumar Kapchorwa, lokacin da motar ta kwace ma direban.
Daga nan motar ta fice daga hanya, ta bugi wani babban dutse a gefen titi sannan ta kife.
'Yan sanda sun bayyana cewa wasu yara da manya da dama sun jikkata, inda aka garzaya da su asibiti domin samun kulawa. Hukumomi sun ce ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin hatsarin.
Uganda na ci gaba da fama da yawan haɗurran ababen hawa, musamman na motocin bas da manyan motoci, sakamakon matsalolin hanyoyi da sauran dalilai.
Hukumomi sun kuma jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu tare da yi wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙi.

0 $type={blogger}:
Post a Comment