Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.4 Ta Auka a Kudancin Mexico.

Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.4 Ta Auka a Kudancin Mexico.

Wata girgizar kasa mai karfin maki 7.4 ta afku a kusa da Puerto Madero da ke jihar Chiapas a kudancin kasar Mexico a ranar Juma'a, kamar yadda Hukumar Kula da Yanayin Kasa ta Amurka (USGS) ta bayyana.

Rahoton ya ce girgizar ta faru ne a zurfin kilomita 10, lamarin da ya sa aka ji karfinta a sassa da dama na yankin.

Ya zuwa yanzu, babu rahoton mutuwa ko jikkata ko gagarumar barna, yayin da hukumomi suka fara tantance irin tasirin da girgizar ta yi. 
An kuma sanya jami'an agajin gaggawa cikin shirin ko-ta-kwana tare da gargadin jama'a su kasance cikin taka-tsantsan saboda yiwuwar sake afkuwar ƙananan girgizar kasa.

An kuma ruwaito cewa an ji girgizar a wasu sassan kasashen Guatemala da El Salvador, amma babu rahoton wata babbar barna a wadannan kasashe.

Hukumomin Mexico na ci gaba da sa ido kan lamarin, kuma ana sa ran za su fitar da karin bayani yayin da ake tattara cikakkun bayanai.

0 $type={blogger}: