Gwamnatin Jihar Jigawa ta sanar da haramta gudanar da bukukuwan yaye dalibai da duk wasu irin bukukuwa makamantansu a dukkan makarantun sakandare na gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar.
Hukumar Kula da Ilimin Manyan Makarantun Sakandare ta Jihar Jigawa (JSSSEB) ta bayyana cewa an dauki wannan mataki ne domin dakile yawaitar jerin gwano ba tare da izini ba da hargitsi a wuraren jama'a da kuma wasu dabi'un rashin da'a da ake dangantawa da bukukuwan yaye dalibai bayan kammala jarabawar karshe ta sakandare.
Hukumar ta umarci shugabannin makarantu da masu makarantu su dakatar da shirya ko halartar duk wani bikin yaye dalibai nan take.
Ta kuma gargadi cewa duk wata makaranta da ta karya wannan umarni za ta fuskanci matakan ladabtarwa da hukunci bisa dokoki da ka'idojin hukumar.
Hukumar ta bukaci dukkan shugabannin makarantu su ba da cikakken hadin kai wajen aiwatar da wannan umarni, tana mai cewa bin dokar zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya, kiyaye doka da oda, tare da inganta tarbiyya da kyawawan halaye a tsakanin dalibai.

0 $type={blogger}:
Post a Comment