Sojojin Amurka Biyu Sun Mutu, Yayin da Ɗaya Ya Bace Bayan Harin Iran a Jordan.

Sojojin Amurka Biyu Sun Mutu, Yayin da Ɗaya Ya Bace Bayan Harin Iran a Jordan.

Sojojin Amurka biyu sun mutu, yayin da aka bayyana cewa wani soja guda ya ɓace bayan wani hari da Iran ta kai a ƙasar Jordan, kamar yadda rundunar sojin Amurka ta sanar.

Lamarin ya faru ne yayin da Yaƙin da ke faruwa tsakanin Amurka da Iran ke ci gaba da ƙamari bayan rushewar yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a baya.

Rundunar CENTCOM ta Amurka ta ce harin ya faru ne a ranar Juma'a, wanda ya ƙara yawan sojojin Amurka da suka mutu tun bayan fara rikicin zuwa 16, yayin da sama da 420 suka samu raunuka.

Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya jajanta wa iyalan sojojin da suka mutu, yana mai cewa sadaukarwar da suka yi za ta ƙara ƙarfafa ƙudurin Amurka.

A nasa ɓangaren, Jagoran addinin ƙasar Iran, Mojtaba Khamenei, ya zargi Amurka da karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta, yana mai gargadin cewa Amurka za ta fuskanci sakamakon ci gaba da tayar da rikicin. 
Ya kuma ce alkawuran Shugaban Amurka Donald Trump ba abin dogaro ba ne.

Rahotanni sun ce Iran ta kai hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa kan wuraren da ke da alaƙa da sojojin Amurka da ƙawayenta a Jordan da Kuwait da Bahrain. 
Kafofin yaɗa labaran Iran sun kuma yi ikirarin cewa an kai hare-hare kan wasu wuraren soja a Saudi Arabiya, sai dai gwamnatin Saudiyya ba ta tabbatar da hakan ba.

A gefe guda kuma, rundunar sojin Amurka ta ce ta ci gaba da kai hare-haren sama a kan wuraren sojin Iran na tsawon kwana bakwai a jere, inda ta kai farmaki kan cibiyoyin sa ido da wuraren adana makamai da cibiyoyin dabarun soja.

Rikicin da ke ci gaba ya ƙara tayar da hankalin duniya game da tsaron yankin Gabas ta Tsakiya da kuma tasirin da zai iya yi ga kasuwannin makamashi, musamman saboda muhimmancin mashigar ruwa ta Hormuz wajen jigilar mai zuwa kasuwannin duniya.

0 $type={blogger}: