Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun sace wasu mutane 'yan uwan juna su uku yayin da suke kan hanyarsu daga Abuja zuwa Jihar Benue domin kai gawar mahaifiyarsu zuwa garinsu don yi mata jana'iza.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Asabar a kan hanyar Ogobia–Otukpo, tsakanin kauyukan Omutele da Ankpechi, a Karamar Hukumar Ohimini ta Jihar Benue.
Majiyoyi sun bayyana cewa motar da suke ciki ta samu matsalar inji a hanya, lamarin da ya jinkirta tafiyarsu har zuwa da misalin karfe 2:00 na dare. Bayan an gyara motar, suka ci gaba da tafiya saboda sun kuduri aniyar kai gawar mahaifiyarsu gida domin a binne ta.
An ce suna ci gaba da tuntubar 'yan uwansu ta wayar tarho har zuwa lokacin da suka isa wurin da aka yi musu kwanton bauna.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun yi awon gaba da 'yan uwan uku tare da dauke gawar mahaifiyarsu zuwa cikin daji. Har yanzu ba a san inda suke ba.
Shugaban Karamar Hukumar Ohimini, Gabriel Adole, ya tabbatar da samun rahoton lamarin, yana mai cewa ya nufi yankin domin tantance abin da ya faru.
A lokacin hada wannan rahoto, rundunar 'yan sandan Jihar Benue ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba, saboda ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ba.

0 $type={blogger}:
Post a Comment