Gwamnan Jigawa Ya Dakatar da Aikin Gyaran Asibitin Gumel na Naira Biliyan 1.3 Saboda Rashin Ingancin Aiki.

Gwamnan Jigawa Ya Dakatar da Aikin Gyaran Asibitin Gumel na Naira Biliyan 1.3 Saboda Rashin Ingancin Aiki.

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya dakatar da aikin gyarawa da sake fasalin Babban Asibitin Gumel mai darajar naira biliyan 1.3 bayan ya gano cewa aikin ba ya tafiya da ingancin da gwamnati ta tanada.

Gwamnan ya dauki wannan mataki ne bayan wata ziyarar bazata da ya kai asibitin cikin dare a ranar Juma'a, inda ya bayyana rashin gamsuwarsa da yadda aikin ke gudana da kuma zargin amfani da kayan gini marasa inganci.

Ya ce abin da ya gani bai yi daidai da abin da gwamnati ta bayar da umarni a aiwatar ba, yana mai jaddada cewa manufar aikin ita ce cikakken gyara da sake fasalin asibitin domin inganta ayyukan lafiya.

Saboda haka, Gwamna Namadi ya ba da umarnin dakatar da aikin gaba ɗaya, yana mai cewa gwamnatin jihar ba za ta amince da aikin da bai kai matsayin inganci ba.

An bai wa kamfanin Yasmeen Automobile Nigeria Limited kwangilar aikin ne a watan Disamban bara, tare da wa'adin kammala shi cikin watanni takwas.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnati za ta zauna da kamfanin domin tattauna matsalolin da aka gano kafin a yanke hukunci kan makomar aikin.

Matakin ya jawo martani daga al'ummar jihar, inda da dama suka yaba da sa ido da gwamnan ke yi kan ayyukan gwamnati. Wasu kuma sun bukaci ya kai irin wannan bincike zuwa sauran asibitocin da ake gyarawa a fadin jihar, musamman Asibitin Gwaram, inda ake zargin aikin da ake yi a can ma ba shi da inganci.

Ba wannan ne karo na farko da Gwamna Namadi ke daukar mataki kan ayyukan da ba su cika ka'ida ba. 
A shekarar 2025, ya umarci a sake aiwatar da aikin magance kwararowar ruwan sama na naira biliyan 10.8 bayan gano amfani da kayan aiki marasa inganci.

0 $type={blogger}: