'Ya'yan Tsohon Mataimakin Gwamnan Bauchi, Sanata Baba Tela, Sun Rasu a Hatsarin Mota

'Ya'yan Tsohon Mataimakin Gwamnan Bauchi, Sanata Baba Tela, Sun Rasu a Hatsarin Mota

Mustapha Baba Tela da Ummi Baba Tela, 'ya'yan tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Baba Tela, sun rasu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su yayin da suke kan hanyarsu ta dawowa Bauchi daga Azare.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Gwamnan Jihar Bauchi Shawara kan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Ƴan Jarida, Comrade Mukhtar Gidado, ya fitar a ranar Asabar, 4 ga Yuli, 2026.

A cewar sanarwar, Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga Sanata Baba Tela da daukacin iyalansa, inda ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga iyali da kuma al'ummar Jihar Bauchi.

Gwamnan ya yi addu'ar Allah Ya jikansu da rahama, Ya gafarta musu kurakuransu, tare da bai wa iyalansu haƙurin jure wannan babban rashi.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa wasu daga cikin mutanen da hatsarin ya rutsa da su na ci gaba da samun kulawa a asibiti, yayin da za a gudanar da jana'izar mamatan a Fadar Sarkin Bauchi da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar Lahadi, 5 ga Yuli, 2026.

0 $type={blogger}: