'Yan Sanda Sun Ceto Wata Mata da Ɗanta Mai Shekaru Biyu Daga Maboyar Masu Garkuwa da Mutane a Jihar Kwara.

'Yan Sanda Sun Ceto Wata Mata da Ɗanta Mai Shekaru Biyu Daga Maboyar Masu Garkuwa da Mutane  a Jihar Kwara.

Rundunar 'Yan Sandan Najeriya ta sanar da ceto wata mata mai shekaru 43 tare da ɗanta mai shekaru biyu daga hannun masu garkuwa da mutane bayan wani samame na musamman da jami'anta suka kai a wani daji da ke yankin Bode Sadu, a Jihar Kwara.

Kakakin rundunar, CSP Aniete Okokon Iniedu, ya ce jami'an Sashen Bayanai na Rundunar (FID-IRT), tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyin tsaro na al'umma, sun kai farmakin ne bayan samun sahihan bayanan sirri kan inda aka tsare waɗanda aka sace.

A cewarsa, masu garkuwar sun bude wa jami'an tsaro wuta da suka hango su, amma jami'an sun mayar da martani cikin dabarun aiki, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa zuwa cikin dajin.

Bayan bincike a yankin, jami'an sun samu nasarar ceto matar mai suna Adijat Kuburat da ɗanta mai shekaru biyu, Abdul Malik Hamzat, daga maboyar masu garkuwar.

Rundunar ta ce an garzaya da mahaifiyar da ɗanta zuwa asibiti domin duba lafiyarsu da kuma ba su kulawar da ta dace.

'Yan sanda sun kuma bayyana cewa ana ci gaba da farautar waɗanda suka tsere domin cafke su tare da rusa ƙungiyar masu garkuwar da ke da hannu a sace mutanen.

Sufeto Janar na 'Yan Sandan Najeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, ya yaba wa jami'an da suka gudanar da aikin bisa jajircewa da ƙwarewa, yana mai jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da yaƙi da masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata manyan laifuka ta hanyar amfani da bayanan sirri da haɗin gwiwa har sai an gurfanar da masu laifin a gaban shari'a.

0 $type={blogger}: